Hebrews 8

Babban Firist na Sabon Yarjejjeniya

1Abin da muke magana a nan shi ne: Muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama, 2wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, wurin kasancewa na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.

3Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yǎ miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yǎ kasance da abin da zai miƙa. 4Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye. 5Suna hidima a cikin wuri mai tsarki wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa saʼad da yana dab da gina Wurin kasancewa cewa: “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
Fit 25.40
6Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakaici ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawarai mafi kyau.

7Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. 8Amma Allah ya sami mutane da laifi
Za a fassara waɗansu rubuce rubucen hannu na dā laifi ya kuma ce wa mutane.
ya ce:

“Ina gaya muku lokaci yana zuwa,
saʼad da zan yi sabon alkawari
da gidan Israʼila
da kuma gidan Yahuda.
9Ba zai zama kamar irin alkawarin
da na yi da kakanni-kakanninsu
saʼad da na kama hannunsu
don in fitar da su daga Masar ba,
domin ba su yi aminci da alkawarina ba,
sai na juya musu baya,
in ji Ubangiji.
10Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Israʼila,
bayan lokacin nan,
in ji Ubangiji.
Zan sa dokokina a cikin zukatansu,
in kuma rubuta su a kan zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
su kuwa za su zama mutanena.
11Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,
balle mutum yǎ ce wa ɗanʼuwansa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin dukansu za su san ni,
daga ƙaraminsu zuwa babba.
12Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”
Irm 31.31-34

13Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.

Copyright information for HauSRK